Majalisa ta amincewa Buhari ciyo bashin N3.65trn

25

Majalisar Dattawa ta amince da bashin kudi dala biliyan 8 da miliyan 300, kwatankwacin naira tiriliyan 3 da biliyan 411, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nema.

Sanatocin sun kuma amince da wani bashin na daban na euro miliyan 490, kwatankwacin naira biliyan 237 da miliyan 851, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nema.

Basukan wani bangare ne na basukan da gwamnatin tarayya za ta ciwo daga shekarar 2018 zuwa 2020.

Majalisar dattawa ta amince da ciyo bashin kudaden bayan tayi la’akari da rahoton kwamitinta mai kula da basuka.

Shugaban kwamitin, Clifford Ordia, ne ya gabatar da rahoton.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Mayu ya bukaci majalisun kasa da su amince da bashin.

Amincewa da bashin, a cewarsa, zai bayar da dama a samu kudaden aiwatar da ayyukan da aka lissafa a shirin basukan da za a ciyo daga shekarar 2018 zuwa 2020.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 20 =