Kwastan a Kano/Jigawa ta tara N12bn a bana

25

Ofishin Hukumar Kwastam na Jihohin Kano da Jigawa ya mika Sabo Suleiman ga Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’anci (EFCC) don cigaba da bincike.

Kwanturolan hukumar, Malam Umar Umar ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Umar ya ce an kame Suleiman dauke da dala 184,800 da Riyal din Saudiyya da miliyan 1.7 a Filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano dake Kano.

Kwanturolan ya cigaba da cewa rundunar ta samar da naira biliyan 12 daga watan Janairu zuwa yau.

Ya kuma ce a cikin watannin, rundunar ta kama buhunan shinkafa 108 na kasashen waje, da katan din sabulu 413, da katan 512 na spaghetti da Jarkokin man girki masu lita 20 guda 83.

Hakanan, Mataimakin Kodinatan Yankin na hukumar ta EFCC, Micheal Nzekwe ya ce hukumar za ta fara bincike kan lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − 4 =