Wata minista ta sayi kadarar $37.5m – Shugaban EFCC

8

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ba da labarin yadda wata minista ta sayi wata kadara ta hannun wani shugaban banki.

Abdulrasheed Bawa yayi magana jiya a wata hira da gidan Talabijin na Channels.

Shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ya bayyana sayen kadarori na gidaje da filaye a matsayin babbar hanyar da ake bi wajen satar kudade.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa EFCC ta binciki wata minista, wacce ta sayi kadara dala miliyan 37 da rabi daga banki sannan ta ajiye tsabar kudi dala miliyan 20.

Shugaban na EFCC, wanda ya boye sunan wacce ake zargin, bai kuma bayyana ko ta kasance minista a yanzu ko tsohuwar minista bace.

Abdulrasheed Bawa ya lura cewa kashi 90 zuwa 100 na dukiyar jama’a da aka sata ana amfani dasu don siyan gidaje da filaye.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven + sixteen =