Buhari yace yaki da rashawa a mulkin demokradiyya na da wahala

13

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace yaki da rashawa a tsarin mulkin siyasa na da wuyar sha’ani sosai.

Shugaban kasar ya sanar da haka a yau yayin da aka yi fira da shi a gidan talabijin na Arise TV.

A cewarsa, yaki da rashawa ya wahalar da shi tun bayan da ya zama zababben shugaban kasa na mulkin demokradiyya shekaru 6 baya.

Sai dai, ya nanata cewa gwamnatinsa ta samu nasarar tumbuke wasu gurbatattun ma’aikatan gwamnati ba tare da yayatawa ba.

Shugaba Buhari ya tunatar da yadda ya samu nasara a yaki da da rashawa a lokacin da yake shugaban kasa na mulkin soja a farkon shekarun 1980.

Shugaban kasar ya bayyana damuwa dangane da yadda ake tafiyar da kananan hukumomi, inda yace a halin yanzu tamkar babu gwamnatocin kananan hukumomi a kasarnan.

A wani batun mai alaka da wannan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk nade-naden mukaman da ya yi, ya dogara ne bisa cancanta ba wai la’akari da kabilanci ko yanki ba.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yau a firar da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV.

A cikin tattaunawar, shugaban ya ce ba zai yi watsi da girman matsayi da cancanta ba, wajen daidaito da raba daidai.

A cikin bayanin nasa, shugaban kasar ya kuma ce ba zai iya fifita wadanda suka yi shekaru kadan a bakin aiki ba kan wadanda suka dade suna aiki.

A wani cigaban mai alaka da wannan, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace rashin aikin yi ga matasa da talauci ne ummul aba’isin rikicin Boko Haram a Arewacin kasarnan.

Shugaba Buhari ya fadi haka a firar da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV wanda aka watsa a yau.

Shugaban kasar yace yayi amannar cewa gwamnatinsa ta taka rawar gani wajen yaki da Boko Haram amma yanayin da ake ciki a Arewa maso Gabas mai wuyar sha’ani ne.

Yace ya yarda cewa mafiya yawan yan Boko Haram ‘yan Najeriya ne, kamar yadda Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulumu ya shaida masa.

Kazalika, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a firar da aka yi da shi, yace gwamnatinsa ta tashi tsaye wajen farfado da hanyoyin shanu da guraren kiwo, a matsayin hanyar magance yawaitar rikicin makiyaya da manoma.

Shugaban kasar ya kuma ce bada dadewa ba ya bukaci gwamnoni biyu na kudu maso yamma, wadanda suka zo domin kawo rahoton hare-hare a kauyukan manoma a jihoshinsu, da su koma jihoshinsu suyi aiki tukuru domin magance rikicin akan suke gudowa zuwa wajensa a Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + 14 =