Da Dumi-Dumi: Anyi arangama tsakanin ‘yan shi’a da ‘yan sanda a Kaduna

179

A safiyar yau Talata ‘yan shi’a suka bijirewa umurnin da ‘yan sanda suka basu na hanasu yin jerin gwano na ranar Asharu kamar yadda suka sabayi duk sheka, inda akaga dandazansu a Abuja.

Amma wasu rahotanni sun nuna cewa mabiya shi’ar sun watse jim kadan da ganin jami’an tsaro don gudun yin arangama dasu, wanda hakan ya haifar da cunkoson ababen hawa a sassa da dama na Abuja.

Sai dai kuma labarin yasha bam-bam a kaduna inda yan shi’an sukayi fito na fito da jami’an tsaron wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane uku, yayin da wasu kuma suka raunata, kamar dai yadda majiyar Sahara Reporters suka ruwaito.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =