Akalla mutane 50 aka kashe a wasu sabbin hare-hare a kudancin kasar jamhuriyar demokradiyyar Congo.
Wata kungiya da ke sa’ido akan rashin tsaro a yankin tace akalla fararen hula 20 aka kashe cikin dare a kauyen Boga kuma an kashe akalla mutane 19 a kauyen Tchabi, wadanda duka suke a lardin Ituru.
Mutanen yankin sun dora alhakin hare-haren akan yan tawayen kungiyar ADF.
Makon da ya gabata, kungiyar ta kashe akalla mutane 22 a lardin North Kivu dake makotaka.
Gwamnatin kasar ta Congo a ‘yan kwanakinan ta kakaba dokar ta baci a dukkan yankunan, inda ta karawa sojoji karfin iko.
Shugaban kasa Felix Tshisekedi ya karawa sojoji karfin iko domin magance rashin tsaro wanda ya haifar da hare-hare da dama kowane mako, duk da kasancewar akwai dubban dakarun zaman lafiya na majalisar dinkin duniya.