Majalisa ta nemi gwamnati ta kawo karshen yajin aikin ma’aikatan shari’ah

27

Majalisar wakilai a yau ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta tabbatar da samar da maslaha dangane da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’ah ke yi.

Wannan ya biyo bayan kudirin da Sergius Ogun na jam’iyyar PDP daga jihar Ondo, ya gabatar a zauren majalisar.

Sergius Ogun, a lokacin da yake gabatar da kudirin, yace bangaren shari’ah na da matukar muhimmanci a gwamnati, kasancewar shi ke da alhakin sasanta rikici wanda ke taimakawa wajen tafiyar da ayyukan gwamnati.

Yace rufe kotunan na matukar barazana ga halin da ake ciki kuma zai iya munana halin rashin tsaron da kasarnan ke ciki.

Sergius Ogun yace yajin aikin ya jawo cunkoso a guraren ajiye mutane na yansanda da gidajen yari a fadin kasarnan, inda ya kara da cewa fursunoni basa samun damar zuwa shari’ah ko samun beli saboda yajin aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 + 4 =