Hare-haren Isra’ila ya raba Falasdinawa 42,000 da gidajensu

121

Falasdinawa kusan 42,000 a Zirin Gaza sun tsere daga gidajensu saboda hare-hare ta sama da Isra’ila ke kaiwa yankin da ke gabar teku.

Sun nemi mafaka a makarantu 50 da ke karkashin kulawar ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Zirin Gaza, in ji mai magana da yawun ofishin a yau.

Ofishin ya kara da cewa fiye da mutane 2,500 sun rasa matsuguni bayan an rusa gidajensu.

Isra’ila ta ce tana kai hare-hare ne a wuraren da ‘yan bindiga suke, amma wasu daga cikin wuraren suna tsakiyar unguwannin dake makare da mutane.

A cewar Isra’ila, sojoji na yin duk abin da za su iya don kaucewa asarar rayukan fararen hula.

Akalla mutane 198 a Gaza, ciki har da yara 58, aka kashe tun bayan barkewar rikicin kimanin mako guda baya, a cewar ma’aikatar lafiyar Gaza.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 4 =