
Shugabannin wasu kasashen Afirka na wani taro a kasar Faransa don tattaunawa a kan hayoyin farfado da tattalin arzikin nahiyar, bayan galabaitar da yayi daga annobar korona.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ne ya shirya taron, inda wasu shugabanni daga nahiyar Turai da wasu hukumomi da cibiyoyin kudi, irin su bankin duniya ke halarta.
Tuni dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Paris domin halartar taron.
A cewar kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, taron zai jawo hankalin manyan masu zuba jari a harkokin kudin duniya wadanda zasu tattauna a tare dangane da samar da kudade da kula da basukan da ake bin Afrika da garabawul ga kamfanoni masu zaman kansu.
Yace Shugaba Buhari zai samu rakiyar ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, da ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, da ministan kasuwanci da zuba jari Adeniyi Adebayo, da ministan lafiya Osagie Ehanire.
Kazalika a cikin ayarin akwai mai bayar da shawara kan tsaro na kasa, Babagana Mohammed Monguno da darakta janar na hukumar leken asiri, Ahmed Abubakar.