ICPC ta ayyana neman surikin Shugaba Buhari ruwa a jallo saboda zamba

33

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta ayyana Gimba Yau Kumo, daya daga cikin sirikan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin almundahanar kudi dala miliyan 65 na kudaden samar da gidaje ga ma’aikata

A shekarar 2016 ne Kumo, tsohon daraktan gudanarwa na bankin samar da gidaje na tarayya ya auri ‘yar shugaba Buhari a Daura da ke jihar Katsina.

Cikin wani jadawali da hukumar ta ICPC ta fitar, ta bayyana Kumo tare da Tarry Rufus da Bola Ogunsola a matsayin wadanda take nema ruwa a jallo saboda zargin tafka almundahana.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin ICPC, Azuka Ogugua, hukumar ta bukaci jama’a su gabatar mata da duk wasu bayanai da za su taimaka mata wajen gano inda mutanen suke.

Hukumar tace duk wanda yake da wani bayani kan inda mutanen suke yana iya ba da rahoto ga helkwatar ICPC da ke Abuja ko ofisoshinta na jihoshi ko ma duk wani ofishin yansanda da ke kusa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + four =