Wadanda aka kashe a Gaza sun karu zuwa 122 inda Falasdinawa ke gujewa hare-haren Isra’ila

30

A yau Isra’ila ta cigaba da yin ruwan bama-bamai a Zirin Gaza da hare-hare ta sama da bindigogin igwa yayin da ta kara tura dakaru da tankokin yaki kusa da yankin Falasdinawa da aka yiwa kawanya.

Akalla Falasdinawa 122, ciki har da yara kanana 31, aka kashe sannan sama da 900 suka samu raunuka tun bayan barkewar fadan a ranar Litinin. Daruruwan Falasdinawa sun nemi mafaka a makarantun da ke karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya a Arewacin Gaza don gujewa luguden wutar Isra’ila.

Duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi na a dakatar da duk wani tashin hankali ba tare da bata lokaci ba, ciki har da shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin cigaba da kai harin.

Hamas ta sake harba wasu rokoki zuwa Isra’ila, inda suka afkawa garin Ashkelon da sanyin safiyar yau.

A wani lamarin da zai kara dumama yanayin siyasa, an harba rokoki akalla uku daga kudancin kasar Lebanon zuwa Isra’ila.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − ten =