Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu domin bikin Karamar Sallah

26

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 12 da Alhamis, 13 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutu don bikin Sallah Karama na bana.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, yayin gabatar da sanarwar a madadin Gwamnatin Tarayya, ya taya Musulmin murnar wannan rana tare da yin kira ga dukkan ‘yan Najeriya, a gida da waje da su yi amfani da lokacin bikin Sallah Karama na bana don yin addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali da karuwar tattalin arziki a kasa.

Aregbesola wanda ya yi imanin cewa cigaba ba zai bunkasa a yanayi mara kyau ba, ya bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su kasance masu bin doka da oda tare da rungumar kaunar juna, ladabtar da kai, kyautatawa da kuma hakuri, kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.

Ya kuma yi kira ga dukkan hukumomin tsaro a kasarnan da su kara jajircewa da kishin kasa don shawo kan yakin da ake yi da rashin tsaro da ayyukan masu tayar da zaune tsaye a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − fifteen =