Mutane 53 dake cikin jirgin ruwan yaki sun mutu a Indonesiya

184

An gano jirgin ruwan yakin kasar Indonesiya ya tarwatse a cikin ruwa a kusa da ruwan Bali, a hukumar soji a yau, bayan ta tabbatar da mutuwar dukkan mutane 53 dake cikin jirgin.

Masu aikin ceto sun gano wasu sabbin abubuwa, gami da rigar ruwa, wadanda suka yi imanin mallakin wadanda ke cikin jirgin ruwan ne mai shekaru 44, wanda yayi batan dabo.

Jirgin ruwan na yaki, daya daga cikin biyar irinsa a jiragen ruwan Indonesiya, ya bace daga tsibirin Bali na kasar ta Indonesiya.

Mahukunta sun ce sun samu sakon signal daga wurin da ke da zurfin mita 800 da sanyin safiyar yau kuma sun yi amfani da wata motar ceto ta cikin ruwa da kasar Singapore ta samar.

Shugaban sojan kasar Marshal Hadi Tjahjanto ya fadawa manema labarai cewa an gano wasu sassan jirgin a yau, ciki har da kayan kariya da rigar ruwan da ma’aikatan jirgin ke sanyawa.

Shugaban Kasa Joko Widodo tun da farko ya tabbatar da gano jirgin ruwan yakin a Tekun Bali ya kuma aika da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − thirteen =