Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da mutane 35 tare da jikkata wani guda yayin da wasu ‘yan fashi da makami suka yi awon gaba da shanu da ba a san adadin su ba, yayin wani hari a kauyukan Chiri Boda da Fuka da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Harin na baya-bayan nan, a cewar majiyoyi daga yankin, ya faru ne a jiya.
Yawancin mazauna kauyukan sun tsere zuwa daji don neman tsira.
Shugaban kungiyar mutanen jihar Neja, Muhammad Awaisu Wana ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar.
Muhammad Wana, wanda yace a halin yanzu mazauna yankin na cikin tsananin damuwa da fargaba, ya koka kan yadda a yanzu gundumomi 10 cikin 15 a karamar hukumar Shiroro ke karkashin ikon ‘yan fashin daji.
Ya kuma ce 8 daga cikin sassan da ke karkashin ikon ‘yan fashin dajin suna yankunan gabar kogi.