Gwamnatin Jigawa za ta dauki ma’ikatan jinya da unguzoma aiki

130

Gwamnatin jihar Jigawa zata dauki ma’aikatan jinya da ungozoma aiki domin tura su zuwa cibiyoyin lafiya a fadin jiharnan.

Shugaban Ma’aikata na Jiha, Hussaini Ali Kila, ya sanar da hakan a wajen babban taron da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta jiha ta shirya a Jamiar Tarayya dake Dutse.

Shugaban ma’aikatan wanda ya samu wakilcin daraktan harkokin gudanarwa na ofishin ma’aikata, Ali Sa’ad Dutse, ya yaba da kyakkyawan dangantakar dake wanzuwa a tsakanin gwamnatin jiha da kuma kungiyoyin kwadago.

Yace gwamnatin jiha tana bada alawus na musamman ga ma’aikatan jinya da suke karatu.

A jawabinsa mataimaki na musamman ga gwamnan jiha kan kwadago Comrade Ibrahim Ahmed Kwaimawa ya bayyana cewa ma’aikatan jinya da ungozoma ta jiha tana taka rawar gani wajen cigaban harkokin kiwon lafiya a jiharnan.

Yace gwamnati ta samar da karin makarantun koyon aikin jinya domin inganta harkokin kiwon lafiya a jiharnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + five =