
Kasar Sudan ta ayyana dokar ta baci a jihar Dafur ta Yamma biyo bayan rikicin kabilanci da ya jawo mutuwar akalla mutane 50 da jikkata wasu 150, tare da raba dubban mutane da gidajensu.
A jiya, majalisar dinkin duniya tace akalla mutane 40 aka kashe da jikkata wasu sama da 50 bayan fada ya barke a ranar Asabar tsakanin kungiyoyin Larabawa da na wadanda ba Larabawa ba, yan kabilar Massalit da ke birnin El Geneina.
A cewar hukumar agaji ta majalisar dinkin duniya, anyi ta jin karar harbe-harben bindiga a jiya da yamma a Al Jamarik da Hay Al Jabal.
Majalisar dinkin duniya ta ce sama da mutane dubu 700 ne a yanzu tabarbarewar tsaro ya shafa a yankin, wanda yawanci hukumomi ke amfani da shi a matsayin cibiyar bayar da agaji a lardin.
A watan Janairu, rikici tsakanin yan kabilar da Massalit da Larabawa ya jawo mutuwar akalla mutane 129 da raba sama da mutane dubu 108 da gidajensu.