
Masauratar Saudiyya ta bayyana kudirinta na fadada dangartakarta da Najeriya, zuwa wasu bangarorin tattalin arziki.
Kasashen Najeriya da Saudiyya na da dadadden tarihin dangantaka wacce ta shafe shekara da shekaru.
Dukkan kasashen biyu, mambobi ne na kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC).
Kazalika, Saudiyya na bayar da tallafin karatu ga daliban Najeriya domin karatu a kasar ta saudiyya.
Duk da kasancewar alaka tsakanin kasashen biyu tafi karfi a bangaren aikin Hajji, inda dubban musulman Najeriya ke zuwa kasar kowace shekara domin Hajji da Umara, Saudiyya tace a shirye take ta fadada dangartakar zuwa wasu bangarori masu muhimmanci, da suka hada da aikin gona, da mai da iskar gas.
Jakadan Saudiyya a Najeriya, Faisal Ibrahim Al-Ghamdi, ya sanar da haka a lokacin zantawa da manema labarai a Abuja.