Majalisa ta rantsar da sabuwar gwamnatin hadin kai a Libya

62

Majalisa ta rantsar da sabuwar gwamnatin hadin kai ta kasar Libya, lamarin dake nuni da karshen gwamnatoci biyu dake adawa da juna tsawon shekaru.

Fira-Ministan wucin gadi, Abdul Hamid Dbeibah, wanda aka zaba a a lokacin zaman tattaunawar neman zaman lafiya da majalisar dinkin duniya ta jagoranta a watan da ya gabata, shine zai jagoranci kasar har zuwa zaben da aka shirya yi a watan Disamba.

Kasar Libya ta fada cikin rikici tun bayan tumbuke Muammar Gaddafi, shekaru 10 da suka gabata.

Daga baya kasar ta rabu tsakanin gwamnatin da majalisar dinkin duniya ke marawa baya a yammacin kasar, wacce ke yaki da jagoran yan tawaye, Khalifa Haftar, wanda gwamnatinsa ta adawa ke rike da iko da gabashin kasar.

Bangarorin biyu suna samun goyon bayan shugabannin yankuna daban-daban.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × two =