NLC ta umarci ma’aikata a jihohi 18 su tafi yajin aiki saboda mafi karancin albashi

24

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta umarci ma’aikatan jihoshi 18 da har yanzu ba a fara aiwatar da mafi karancin albashi na naira dubu 30 ba, da suyi gaggawar tafiya yajin aiki.

Kungiyar tace har yanzu kimanin rabin jihoshin Najeriya 36 basu kammala tattaunawa ba dangane da biyan mafi karancin albashin.

Bincike yayi nuni da cewa jihoshin da basa biyan mafi karancin albashin sun hada da Imo, Rivers, Osun, Ekiti, Ebonyi, Kwara, Zamfara, Gombe, Rivers da Ogun.

Umarnin tafiya yajin aikin na kunshe cikin sanarwar bayan taro da aka fitar a karshen taron majalisar zartarwar kungiyar ta kasa.

Kungiyar ta kuma bukaci a sake bibiyar tsarin farashin man fetur domin magance karin farashin man da ake tsammani, biyo bayan karin farashin danyen man a kasuwannin duniya.

Ta kuma umarci gwamnatin tarayya ta rage farashin gas din da take sayarwa kamfanonin samar da wutar lantarki da nufin samun ragin kudin wutar lantarki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × five =