Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin hanyar jirgin kasa daga Najeriya zuwa Nijar

48

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau yayi bikin aza tubalin gina titin jirgin kasa daga Kano zuwa Dutse zuwa Jibia zuwa Maradi mai tsawon Kilomita 284 wanda zai hada Kano a Najeriya zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Aikin na dala biliyan 1 da miliyan 960 ya sami sahalewar zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya, wanda shugaban kasa ya jagoranta a watan Satumba, 2020.

Aikin, wanda aka yi amannar yana da mahimmanci ga cigaban sufurin jiragen kasa a Najeriya da yankin Afirka ta Yamma, kamfanin rukunin Mota-Engil ne zai aiwatar da shi.

Aikin wanda zai samar da tashoshi 15 a kan hanyar, ana sa ran kammala shi a cikin shekaru uku masu zuwa kuma zai bunkasa tattalin arziki a jihoshin Kano, Katsina da Jigawa a Najeriya da kuma Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a ranar 11 ga watan Janairu ya sanar a shafin twitter cewa dan kwangilar ya amince zai gina jami’a a matsayin wani bangare na ayyukan cigaban al’umma na kamfanin yayin da ake aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × four =