Fadar Shugaban Kasa ta kare Buhari dangane da cire takunkumi a bainar jama’a

53

Fadar Shugaban kasa a yau ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai karya ka’idojin corona ba a Daura, Jihar Katsina, a karshen mako.

Hotunan internet sun nuna yadda Buhari ke tattaunawa da wasu gwamnonin jam’iyyar APC yayin sabunta rijistar jam’iyyar ta APC a garin Daura a ranar Asabar ba tare da sanya takunkumin rufe fuska ba ko kuma bai wa juna tazara kamar yadda yake a sabuwar dokar ka’idojin kariya daga corona ta bana, wacce ya sanyawa hannu.

Jam’iyyar PDP da ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun caccaki shugaban kasar saboda sabawa ka’idojin da suka sanya yin amfani da abin rufe fuska a bainar jama’a ya zama tilas a cikin sauran matakan takaita yaduwar COVID-19.

Ka’idojin sun kuma tanadi biyan tarar kudi ko daurin watanni shida ko duka biyun ga wanda aka kama ya taka dokar.

Da yake magana a yau, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da huldar jama’a, Malam Garba Shehu, ya ce shugaban kasar na sanye da abin rufe fuska a wajen rijistar amma ya cire lokacin da yake magana.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × four =