Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara, Farfesa Magaji Garba ya shiga hannun Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC).
Hukumar ta tsare shi a ranar Alhamis din da ta gabata bayan ya amsa gayyatar da tayi masa dangane da hannunsa wajen cin amanar aiki da cin hanci da rashawa, da kuma damfara.
Wata majiya mai karfi a hukumar ta EFCC ta bayyana cewa Mataimakin Shugaban Jami’ar, a wani lokaci a cikin shekarar 2018, ya damfarar kudi Naira miliyan 260 daga hannun wani dan kwangila mai suna Alhaji Shehu Sambo, mai kamfanin Ministaco Nigeria Limited, bisa dalilin cewa jami’ar za ta bai wa kamfaninsa kwangila ta kimanin naira biliyan 3 don gina katangar jami’ar.
Amma kwangilar ba ta samu ba lamarin da ya sa Shehu Sambo ya nemi aiki da korafi zuwa ga hukumar EFCC.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da kamen ga manema labarai a yau amma bai ba da karin haske ba.