Gwamnan Ondo ya bawa makiyaya wa’adin kwana 7 su fice daga dazuka

86

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bai wa makiyaya kwana bakwai su bar dazukan jihar.

Gwamna Akeredolu ya bai wa makiyaya wannan wa’adi a yau lokacin da yake ganawa da al’ummar Hausa/Fulani da Ebira dake jihar.

Gwamnan bayyana cewa Funali ne sanadin galibin sace-sacen mutanen da ke faruwa a jihar tasa.

Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa nan babban mai kula da sha’anin tsaro na jiharsa, ba zai zuba ido ba ya bari ana cigaba da aikata irin wadannan laifuka.

A cewarsa, sun dauki matakin ne da zummar tabbatar da tsaron rayuka da na kaddarori a jihar ta Ondo yana mai bayar da umarni ga jami’an tsaro su tabbatar da an aiwatar da dukkan umarnin da ya bayar.

Ya kuma haramtawa yara kiwon dabbobi tare da haramta zirga-zirgar shanu a cikin birane da manyan tituna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − six =