Gwamnatin Tarayya a jiya ta hana cunkoson mutane da manyan taruka da kuma ziyarar dalibai, kasancewar za a sake bude makarantu a ranar Litinin mai zuwa.
Hakanan ya iyakance yawan dalibai a aji da dakunan kwanan dalibai kuma ta nemi makarantu da su tabbatar da cewa dalibai da malamai da ma’aikata na sanya takunkumin fuska, tare da tabbatar da binciken zafin jiki da samar da wuraren wanke hannu a wurare masu mahimmanci a duk makarantun.
Gwamnati ta kuma nemi mahukuntan makarantun da su tabbatar da samar da ruwa da tsaftar mahalli a koyaushe, sannan a samar da asibitocin kiwon lafiya masu aiki tare da wuraren killace mutane da jigilar wadanda ake zargi sun harbu da cutar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya bayar da wadannan sharuddan a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Ben Bem Goong ya fitar. Adamu ya fadawa iyayen yara da kuma makarantun da su tabbatar sun cika dukkan ka’idojin kariya daga cutar corona.