Shugabannin kwadago sun fice daga ganawa da gwamnati akan karin kudin mai

25

Wakilan kungiyoyin kwadago sun fice daga wajen zaman ganawa tare da gwamnatin tarayya a ranar Lahadi.

Kungiyoyin kwadagon sun fice daga wajen zaman kasa da mintuna biyar da fara ganawar.

Shugaban Kungiyar kwadago ta TUC, Quadri Olaleye, ya gayawa manema labarai cewa karin farashin man fetur da karin kudin wuta sune manyan dalilan zaman ganawar, ba wai batun kayan tallafi ba.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, shi ne ya wakilci gwamnatin tarayya tare da karamin ministan kwadago da aikin yi, Festus Keyamo, da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, da karamin ministan wuta, Goddy Agba, da kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − 13 =