Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya mutu sanadiyyar cutar corona

46

Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya mutu yana da shekaru 73 a duniya, sanadiyyar cutar corona.

Mutuwarsa tazo kasa da wata guda bayan ya binne mahaifiyarsa da ta rasu.

Jerry Rawlings, wanda daya ne daga cikin shugabannin Afirka da ake girmamawa, tsohon shugaban kasar Ghana ne na mulkin soja wanda daga baya ya zama dan siyasa, kuma ya mulki kasar daga shekarar 1981 zuwa 2001.

Tsohon shugaban kasar tunda farko ya zama shugaban kasar Ghana a matsayin sojan sama, bayan juyin mulkin shekarar 1981.

Kafin nan, ya jagoranci yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba akan gwamnatin soja mai ci a ranar 15 ga watan Mayun 1979, makonni kalilan kafin zaben da aka shirya ya gudana.

Kafin rasuwarsa, shine jakadan kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somalia.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + 15 =