Gwamnatin Kaduna zata fara karbar harajin N1,000 kowace shekara daga kowane baligi

14

Hukumar tara kudaden shiga ta jihar Kaduna tace zata fara aiwatar da shirinta na karbar naira dubu 1 daga dukkan baligin dake zama a jihar a matsayin harajin cigaba, a shekara mai zuwa.

Shugaban hukumar, Dr Zaid Abubakar ya fada a wajen taron manema labarai ranar Laraba a Kaduna cewa daga shekara mai zuwa, duk wani baligin dake zama a jihar zai biya harajin a karkashin tanadin sashe na 9, 2 a cikin baka na dokar harajin jihar Kaduna ta bana.

Ya kara da cewa dokar ta bukaci duk wani baligin dake zaune a jihar da ya biya naira dubu 1 kowace shekara a matsayin harajin cigaba, wanda gudunmawarsa ce wajen gyara da samar da ababen more rayuwa tare da habaka tattalin arziki domin biyawa jama’a bukatunsu.

Zaid Abubakar yace harajin yana karkashin tanadin kundin tsarin mulki wanda ya bawa jihoshi damar karbar adadin kudi a kowace shekara daga mazauna jihar a matsayin harajin cigaba ko harajin cigaban tattalin arziki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × two =