Gwamnatin Tarayya za ta sayar da NNPC

17

Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, yace a kudirin dokar masana’antar man fetur da aka sake gyarawa, baza a soke kamfanin mai na kasa NNPC ba, sai dai za a sayar da shi, akan turbar kokarin mayar da bangaren ya zama mai cin gashin kansa ta kowane fanni.

Ya fadi haka lokacin da yake jawabi ga manema labarai ranar Litinin, bayan wata ganawar hadin gwiwa tare da shugabannnin majalisar kasa.

Ministan ya kuma cigaba da cewa bayan kasancewar al’umomin da ake hakar mai a wajensu za suci moriyar kudirin sosai, za a yiwa masana’antar garanbawul, kuma za a canja tsarin hukumar asusun man fetur da hukumar kayyade farashin albarkatun man fetur, daga yadda suke a yanzu.

Yayin ganawa da shugabannin majalisar kasa, Timipre Sylva ya kambama bukatar dake akwai ta gaggauta zartar da kudirin domin samun gagarumar riba a bangaren kafin shekarar 2040.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, duk sunyi alkawarin gaggauta zartar da kudirin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 14 =