Dalilinmu na fasa tafiya yajin aiki da zanga-zanga – Gamayyar kungiyoyin kwadago

68

Gamayyar kungiyoyin kwadago karkashin wakilcin kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC sun bayar da dalilan da suka sanya su janye tafiya yajin aiki da zanga-zangar da aka shirya gudanarwa.

Sun sanar da haka a wata takardar bayan taron da suka saki, wacce wakilinmu ya sama a yau.

A madadin gamayyar kungiyoyin kwadagon, takardar bayan taron na dauke da sa hannun shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba, da shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Quadri Olaleye da Babban Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja da Babban Sakataren TUC Musa Lawal Ozigi, da sauransu.

A cewar jagororin kungiyoyin kwadagon, sun yi la’akari da illar cutar corona kafin su amince da janye tafiya yajin aikin.

Sun kuma yi nuni da cewa gwamnatin tarayya ta yi musu bayani dangane da halin da tattalin arziki ke ciki da kuma dalilin da yasa aka kara kudin wuta tare da janye tallafin man fetur.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − eleven =