Shugaban Kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo ya ambaci sunan Mohamed Hussein Roble a matsayin Firai-Minista.
Shugaban kasar yace an zabi Roble bisa la’akari da iliminsa da kwarewarsa da kuma damar da yake da ita wajen kawo cigaba da samar da tsare-tsaren gina kasa.
Idan Hussein Roble ya samu amincewar majalisar, zai maye gurbin Hassan Ali Kaire, wanda aka tumbeki bayan samun rashin goyon bayan majalisa a ranar 25 ga watan Yuli.
Shugaban Kasa Farmajo, a cikin wata sanarwa ya bukaci Firai-Ministan mai jiran gado da ya gaggauta kafa gwamnatin da zata kai kasar zuwa zabe tare da yin hobbasa wajen sake gina dakarun soji da samar da gine-gine da kuma fadada samar da abubuwan rayuwa.
Firai-Ministan mai jiran gado, sabon shiga ne a siyasar Somaliya.