Fira Ministan Libya al-Serraj yace zai sauka daga mulki a Oktoba

20

Firaminista Fayez Al Serraj na Libya ya ce yana shirin mika mulki ga wata sabuwar gwamnatin da ake sa ran za ta fara aiki a karshen watan Oktoba.

Mista Serraj ne ke shugabantar gwamnatin da majalisar dinkin duniya ke marawa baya a Tarabulus, babban birnin kasar.

A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin a jiya Laraba, Firaministan ya nemi kwamitin da ke shirya zaman sasancin da za ayi a Geneva wata mai zuwa, da ya hanzarta kafa sabuwar majalisar ministoci da za ta maye gurbin gwamnatinsa domin a sami mika mulki cikin sauki.

Al-Serraj na shan matsi dangane da suka daga bangarorin dake cikin Gwamnatin Tarabulus da kuma zanga-zangar baya-bayan nan akan kuncin rayuwa da rashawa a gwamnati.

An nada shi a matsayin Fira-Minista kuma shugaban majalisar kasar Libya a karkashin wata yarjejeniyar da majalisar dinkin duniya ta shirya wacce aka sanyawa hannu a kasar a watan Disambar 2015.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + 9 =