Najeriya na kan gabar tarwatsewa gabadaya – Soyinka

49

Fitaccen marubucin nan wanda ya taba lashe lambar Nobel, Wole Soyinka, yace yan Najeriya sun cire tsammani daga gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a matsayin wacce ta jajirce wajen tabbatar da dorewar kasarnan a matsayin kasa guda.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya, Soyinka yace yan Najeriya sun dena yarda cewa gwamnatin ta fahimci mafi kankantar abinda ake bukata wajen dora kasarnan a turbar cigaba.

Sukar ta Wole Soyinka tazo kwanaki kadan bayan tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo yayi gargadin cewa sannu a hankali kasarnan na kokarin kasawa, ta kuma dare, sannan ta zama cibiyar talaucin duniya.

A martanin da ta fitar, fadar shugaban kasa ta soki Obasanjo, inda ta bayyana shi da babban mai raba kan jama’a na kasa.

Soyinka yace duk da kasancewar baya goyon bayan Obasanjo, ya yarda da shi cewa Najeriya na kan gabar tarwatsewa gabadaya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + five =