Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yace bazai bata lokaci ba wajen sanya hannu akan hukuncin kisa da babbar kotun shari’ar musulunci ta Kano ta yankewa mawakin nan, Yahaya Sharif, bisa laifin yin batanci ga fiyayyen halitta.
Gwamna Ganduje ya sanar da haka a wani taron masu ruwa da tsaki dangane da lamarin, a gidan gwamnati dake Kano.
Ganduje yayi nuni da cewa wanda aka zartarwa da hukuncin, yana da wa’adin kwanaki 30 domin ya daukaka kara, inda ya kara da cewa idan kwanaki talatin din suka kare bai daukaka karar ba, bazai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya hannun akan a zartar masa da hukuncin.
Ganduje ya bayyana takaicin yadda annobar batanci ga fiyayen halitta ke dada karuwa a yan kwanakinnan, inda ya jaddada cewa gwamnati baza ta saurara ba har sai ta magance matsalar.
Ya yabawa malaman addinin musulunci bisa jajircewarsu wajen tabbatar da cewa an hukunta mai laifin daidai da abinda ya aikata.