Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace inganta ayyukan hakar zinare a kasarnan zai samar da ayyukan yi dubu dari biyu da hamsin tare da Dalar Amurka sama da miliyan dari biyar kowace shekara a matsayin kudaden shiga ga gwamnatin tarayya.
Ya kuma ce kasar tana asarar kimanin dala biliyan uku ga masu fasa kwaurin zinaren tsakanin shekarar 2012 zuwa 2018.
A cewar wata sanarwa ta hannun mai bashi shawara na musamman akan kafafen yada labarai da huldar jama’a Femi Adesina, shugaban kasa ya sanar da haka a wajen gabatar da zinaren da aka hako a kasarnan wanda shirin inganta hakar zinare na shugaban kasa yayi a Abuja.
An ce shugaba Buhari a wajen gabatarwar ya kuma jaddada jajircewar gwamnatinsa wajen assasa guraren sarrafa danyen zinare a Najeriya.
Yace shirin zai agazawa kokarin samar da ayyukan yi ga yan Najeriya da fadada hanyoyin shigowar kudade tare da inganta ma’adanar kudaden waje.