Shugaba Buhari yayi kiran neman hadin kai tsakanin kasashe domin yaki da Corona

28

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace illar da annobar corona ta yiwa tattalin arziki da walwalar jama’a, ya sanya kasashe da dama baza su iya jurewa ba.

Shugaba Buhari yace annobar ta shafi tsarin kiwon lafiyar kasashe da dama.

Shugaban Kasar ya fadi haka cikin wata sanarwa da ya gabatar wajen taron China da kasashen Afirka domin taimakawa a yaki da cutar corona, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar kungiyar hadin kan China da Afirka.

Shugaba Buhari ya fada a wajen taron wanda Shugaban Kasar China Xi Jinping ya shirya da hadin gwiwar Shugaban Kasar Afirka ta Kudu kuma shugaban kungiyar tarayyar Afirka, Cyril Ramaphosa, da shugaban kasar Senegal kuma shugaban kungiyar hadin kan China da Afirka, Macky Sall, cewa akwai bukatar hadin kai wajen yaki da annobar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 4 =