
‘Yansanda a Ghana sun harbe wani dan Najeriya har lahira lokacin da ake biki a wani Otal.
Mutumin wanda ba a gane ko wanene ba, anyi zargin an bindige shi, lokacin da ‘yansanda ke kokarin tarwatsa mahalarta bikin.
A wani faifan bidiyon da abokin mamacin ya wallafa a shafin YouTube, yayi nuni da cewa an kuma kashe wani mutumin daban, wanda ba a ambaci sunansa ba, yayin hatsaniyar.
A faifan bidiyon, an ga wasu mutane sun dauke wata gawa zuwa asibiti.
Kazalika an ga wata mata a bidiyon, tana jimamin kisan, inda take cewa ‘yansandan Ghana suna kai farmaki kan ‘yan Najeriya a ko da yaushe.
An ga ‘yansanda suna kame mahalarta bikin, suna tafiya da su, ga dukkan alamu saboda taka dokar bawa juna tazara lokacin annobar corona.