Kungiyar NASU Zata Fara Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 14

32

Kungiyar ma’aikatan manyan makarantu wadanda ba malamai ba (NASU) tace zata fara yajin aikin gargadi na kwanaki 14 a dukkan jami’o’in gwamnatin tarayya, da polytechnic, da kwalejojin ilimi, bisa matsalar da aka samu wajen biyan ‘ya’yan kungiyar albashinsu.

Kungiyar tace yajin aikin zai fara daga ranar da aka koma bakin aiki a dukkan makarantun da ta zayyana.

Wannan na zuwa ne watanni 2 bayan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta fara nata yajin aikin.

Kungiyar ta NASU ta shiga yajin aiki na karshe a watan Augustan bara, bisa gazawar gwamnati wajen shawo kan matsaloli wadanda suka hada da tattaunawar yarjejeniyar 2009, biyan alawus-alawus, da sauransu.

A wata sanarwa da aka fitar jiya Litinin da dare, sakataren kungiyar na kasa, Peters Adeyemi, yace ma’aikatan da basa koyarwa suna kalubalantar rashin biyan ‘ya’yan kungiyar cikakken albashinsu tun daga watan Fabrairun bana ta tsarin biyan albashi na IPPIS.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − fifteen =