Gwamnatin Tarayya Ta Karbo Dala Miliyan 311 Wanda Abacha Ya Sace

20

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da karbar kudi dala miliyan 311 wadanda tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya sata daga Amurka da tsibirin Jersey.

Attoni Janar na kasa kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, a wata sanarwa da kakakinsa Dr. Umar Jibrilu Gwandu ya fitar, yace an karbo kimanin dala 311,797,866.11 na kudaden da Abacha ya sace daga Amurka da Jersey.

A cewar Malami, yawan kudaden ya karu daga dala miliyan 308 kamar yadda aka fada a wata sanarwa a watan Fabrairu, zuwa sama da dala miliyan 311, saboda kudin ruwan da ya taru daga ranar 3 ga watan Fabrairu zuwa 28 ga watan Afrilu, lokacin da aka aika da kudin zuwa babban bankin kasa CBN.

Attoni Janar na kasa yayi nuni da cewa an fara shirye-shiryen karbo kudaden a shari’ance tun a shekarar 2014.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + 14 =