Gwamnatin Bauchi Ta Karbi Almajirai 196 Daga Jihar Filato

49

Gwamnatin jihar Bauchi ta karbi kimanin almajirai 196 da aka kwaso daga karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Mataimakin gwamnan jihar ta Bauchi, Sanata Baba Tela, ya karbi almajiran a makarantar hadaka ta Janar Hassan Usman Katsina, a madadin gwamnatin jihar.

Yace za a yiwa almajiran gwajin lafiya tare da sauran gwaje-gwaje, kafin a mika su zuwa ga iyayensu.

Yace gwamnan jihar, Bala Mohammed, ya amince da ajiye Almajiran a makarantar hadakar ta Janar Hassan Usman Katsina dake Yelwa, kafin lokacin da za a tabbatar da lafiyarsu kuma a sada su da iyayensu.

Baba Tela wanda kuma shine shugaban kwamitin karta kwana na jihar Bauchi akan cutar corona da zazzabin Lassa, yace za ayi binciken lafiyar almajiran domin tabbatar da cewa basu kamu da cutar corona ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 4 =