Sakataren Harkokin Wajen Amurka Yace Akwai Yiwuwar Kasar Baza Ta Dawo Da Bawa WHO Kudade Ba

22

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace annobar corona ta nuna bukatar dake akwai na garanbawul a hukumar lafiya ta duniya, WHO, inda yayi gargadin cewa akwai yiwuwar fadar Amurka a Washington baza ta dawo da bawa hukumar kudade ba, kuma zata iya aiki wajen kafa wata hukumar makamanciyar wannan ta majalisar dinkin duniya.

Lokacin da Mike Pompeo yake sake kalubalantar hukumar lafiyar, ‘yan jam’iyyar Democrats a majalisar wakilan Amurka sun zargi gwamnatin Trump da kokarin dorawa hukumar laifi, domin janye hankalin mutanen daga yadda gwamnatin ta yiwa annobar rikon sakainar kashi.

A wata wasika da suka aikawa Shugaba Trump, ‘yan majalisar sunyi kira da a gaggauta dawo da bawa hukumar lafiyar kudaden, wanda shugaba Trump ya dakatar a makon da ya gabata, bayan ya zargi hukumar ta WHO da zama ‘yar amshin shatar China, wacce kuma ke marawa rufa-rufar da China tayi akan annobar baya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + fifteen =