Trump ya tabbatar da aniyarsa ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ƙorar bakin haure

1
Donald Trump

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya tabbatar da aniyarsa  ta ayyana dokar ta-ɓaci a kan ƙorar bakin-haure, waɗanda ba su da takardun izinin zama a ƙasar kamar yadda ya yi alƙawari a yayin yaƙin neman zaɓen sa, inda ya ce zai yi amfani da sojoji wajen tisa ƙeyarsu.

Trump wanda ya tabbatar da haka a yayin da ya ke amsa tambaya daga shugaban gidauniyar Judicial Watch, Tom Fitton ta dandalin sada zumunta, ya ce zai fara tisa ƙeyar bakin hauren ne da zarar ya fara aiki.

A cikin kwanakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓensa, Trump ya sha alwashin ƙaddamar da shirin tisa ƙeyar baƙin-haure mafi girma a tarihin Amurka, inda  ya ce zai ceto dukkan birane da garuruwa da  baƙin su ka wa kutse, su ka kuma mamaye.

Tuni zaɓaɓɓen shugaban ya zaɓi masu tsatsauran ra’ayi a game da kwararar baƙin-haure su kasance daga cikin  ƴan majalisar zartaswarsa, inda gwamnar jihar South Dakota, Kristi Noem za ta kasance sakatariyar tsaron cikin gida idan ta samu amincewar majalisar dattawa, sai kuma tsohon shugaban hukumar shige da fice ta kasar, Tom Homan wanda zai kula da iyakoki.

An ƙiyasta cewa akwai kimanin baƙin-haure miliyan 11 a Amurka, waɗanda ke zaune a ƙasar ba tare da izini ba, kuma kawar da su zai laƙume biliyoyin daloli a duk shekara, a cewar cibiyar kula da shige da fice ta Amurka.

RFI HAUSA

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + one =