Ribadu ya jaddada bukatar daukar matakai a jihar Katsina kan illolin dumamar yanayi a taron COP29 na Majalisar Dinkin Duniya

48

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan jihar Katsina kan abun da ya shafi dumamar yanayi, wato SSA On Climate Change a turance  Suleiman Ribadu, ya jaddada bukatar samar da ingantattun hanyoyin kare muhalli daga illolin dumamar yanayi a jahar Katsina.

Suleiman Ribadu ya yi wannan kiran ne a garin Baku na kasar Azerbaijan inda yake wakiltar gwamnatin jahar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda a taron Majalisar Dinkin Duniya (United Nations) na 29 akan dumamar yanayi (COP29).

Ribadu ya yi kiran ne bayan kammala wani taro na musamman da wasu daga cikin shuwagabannin duniya inda aka tattauna illar da dumamar yanayi take janyowa kasashe da garuruwa masu karamin karfi irin Katsina. 

Illolin sun hada da kwararar hamada, ambaliyar ruwa, fari, noma, canjin yanayi da sauran ire iren su.

Haka zalika ya gayyaci mahalarta taron da su zo jahar Katsina don kawo irin tallafin da ake kawowa masu fama da ire iren wadannan illoli musamman lura da kokarin da Gwamnan Malam Dikko Umar Radda ya ke yi wajen dawo da martabar tattalin arziki ta hanyoyin noma da kiwo, farfado da masana’antu da dai sauran hanyoyin samar da arziki masu dorewa.

Tattaunawar hadimin Gwamnan Suleiman Ribadu tare da sauran ma su ruwa da tsaki a wurin babban taron ta shafi muhimman abubuwa da dama kamar samar da tallafin kuɗi domin gudanar da ayyukan da suke bada gudummawa wajen magance dumamar yanayi, samar da fasaha da kimiyya wajen magance illolin dumamar yanayin da kuma horas da masu ruwa da tsaki da ma alummar jaha akan ayyukan sa kai don taimakawa muhalli da kuma wayar da kan matasa maza da mata da sauran masu ruwa da tsaki. 

“Katsina zata samu tagomashi mai girma sakamakon wannan tattaunawar kuma alheri da yawa yana hanyar shigowa jihar Katsina karkashin jagorancin adalin Gwamna kuma haziƙin, Gwamna Mallam Dikko Umar Radda,” a cewar Suleiman Ribadu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × five =