Yaƙi ya ƙazance tsakanin Rasha da Ukraine

27
Vladimir Putin

Dakarun Ukraine da na Rasha sun ci gaba da kai wa juna farmaki a tsawon dare, mako ɗaya tun bayan da dakarun Ukraine suka kutsa cikin yankin Kursk da ke Rasha.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce garkuwar kare hare-hare ta sama na ƙasar ta lalata jiragen yaƙi marasa matuƙa guda 12 a yankin na Kursk da kuma wasu a yanunan Belgorod da Voronezh.

A nata ɓangaren, rundunar sojin Ukraine ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa 30 da makamai masu linzami biyu mallakin Rasha.

Rahotanni na cewa ana ci gaba da gwabza yaƙi a yankin Kursk, inda Ukraine ke ƙoƙarin faɗaɗa samamen da take yi a Rasha, sai dai ta gamu da turjiya mai tsauri daga dakarun Rasha.

BBC HAUSA

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 4 =