TSOHON MINISTAN SADARWA ADEBAYO SHITTU YACE BA’A GABATAR DA RAHOTAN ORONSAYE GA GWAMNATIN BUHARI BA

10

Tsohon Ministan sadarwa Adebayo Shittu,yace ba’a gabatar da rahotan Steven Oronsaye ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari data gaba ta ba.

Adebayo Shittu,wanda yayi Minista a wa’adin farko na gwamnatin Buhari daga shekarar 2015 zuwa 2023.

A cewar sa, ba’a janyo hankali gwamnati Buhari ga rahotan na Oransaye ba,a don haka babu bukatar yin amfani da shi.

Tun bayan da gwamnatin tarayya ta amince da yin amfani da rahotan na Steve Oronsaye domin rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, aka ta ce-ce-ku-ce.

Ana tsammanin za’a hade hukumomin gwamnatin tarayya a wuri guda,yayinda za’a hade ma’aikatu takwas da hukumomi takwas a wuri guda,hakan yasa fargaba a zukatan wasu ‘Yan Najeriya zasu iya rasa ayyukan su.

Da yake jawabi dangane da wannan lamari Adebayo Shittu, yace bai kamata wani ma’aikacin gwamnati yayi fargabar rasa aikin sa ba, yana mai cewa hakan ‘Yan siyasa kadai zai shafa domin za’a rage wadanda aka baiwa mukamai a gwamnati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × one =