
Shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai ya kafa kwamitin kar ta kwana na yaki da cin hanci da kwato kadarorin kasar da aka sace.
Mista Boakai ya bada umarnin a gano tare da gurfanar duk wani babban ma’aikaci dake da hannu a cin hanci ko satar dukiyar kasar a gwamnatin yanzu da wacce ta shude.
Bisa wannan umarni za’a dawo da duk wata kadarar gwamnati da aka mallaka ba bisa ka’ida ba.
Shugaban kasar yace a hukumce za’a magance matsalolin da suka dabai-baiye kasar.
Kazalika,dukkan wadanda suka sayi kadarar gwamnati ba bisa ka’ida ba zasu dawo da ita.
Dai-dain ‘yan kasar dake zaune a wata da ake zargin sun kwashe dukiyar al’umma za’a maida su gida.
Tuni aka ware kudaden tafiyar da wanna kwamitin wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba.
