SARKIN MUSULMI YA NEMIN SAMUN SAUKIN MATSALOLIN TSARO DA MATSIN RAYUWA DA AKE FUSKANTA A NAJERIYA

15

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh Sa’ad Abubakar na uku, ya ayyana yau Litinin 11 ga watan Maris a matsayin daya ga watan Ramadana.

Sarkin Musulmi,yace an ayyana yau a matsayin watan Ramadan bayan ganin jaririn wata a wasu sassan kasar nan.

Yayi kira ga dukkan musulmi a fadin Najeriya da su fara Azumi a yau bisa koyarwar addinin Islama.

Alh Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi da su yi amfani da watan wajen yin addu’o’I neman magance matsalolin tsaro dake addabar kasar nan.

Kazalika, yayi kira ga Musulmi da su yi amfani da wannan wata wajen yiwa shugabannin addu’o’I  domin sauke nauyin dake kan su.

Alh Sa’ad Abubakar ya shawarci Musulmi su azumci wannan wata da tsoron Allah,yayinda ya bukaci mawadata da suyi amfani da dukiyar su wajen ciyar da marasa galihu musamman a wannan wata mai falala.

A halin da ake ciki kuma,gwaman Jihar Oyo Seyi Makinde,ya taya daukacin Musulmi Najeriya dana duniya baki daya murnar zuwan watan Ramadan mai albarka na wannan shekara ta 1445.

Gwamnan, ya bayyana watan a matsayin mai falala wanda Allah yake baiwa musulmi ladan ayyukan da su ka aikata.

Makinde ya bukaci Musulmi da sukara addu’o’in su ga kasar nan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − ten =