PETER OBI YACE KO KADAN BAI DAMU YA ZAMAN SHUGABAN NAJERIYA BA

13

Dan takarar shugabancin Najeriya na jami’iyyar Labour a zaben shekara ta 2023 Mista Peter Obi, yace ko kadan bai damu da sai ya zama shugaban kasa ba, amma dai burin sa shine ya ga Najeriya ta na kan tafarkin cigaba.

Mista Obi ya furta hakan ne a birnin Abuja a wurin babban taron shekara-shekara kan jagoranci da kuma bada lambobin yabo karo na 16 na shekara ta 2023, inda aka bashi lambar yabo ta zama gwarzon dan siyasa.

Dan takarar shugaban kasar, kuma tsohon gwamnan Jihar Anambara ya bayyana farin cikin sa bisa bashi lambar yabon, inda yace lamari daga Allah madaukakin sarki ne.

Ya kuma jadadda kudirin sa kan burin da ya ke da shi a Najeriya,inda yace muddin aka bashi dama ya zama shugaban kasa zai matukar kokari wajen kawo cigaban kasar nan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − five =