PETER OBI YA BADA TALLAFIN KARATU GA DIRERAB ADAI-DAITA SAHU WANDA YA MAIDA KUDIN TSINTUWA NAIRA MILYAN 15

14

Dan takarar shugabancin Najeriya na jami’iyyar  Labour a zaben shekarar ta 2023 Mista Peter Obi da mataimakin sa na takara Baba Ahmed Datti,ya sanar da bada tallafin karatu ga direban adai-daita sahu Auwalu Salisu,wanda ya maida kudi Naira Milyan 15 ga mai shi.

Idan za’a iya tunawa a watan satumbar da ya gabata ne matukin adai-daita sahun Auwalu Salisu, mai shekaru 22 ya maida kudin Naira Milyan 15 ga mai shi, wanda ya manta su a cikin a dai-daita sahun da yake tukawa.

Auwal Salisu, mazaunin unguwar Yankaba a yankin karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano,ya maida kudi bayan yaji sanarwar cikiya kudaden a gidan Rediyon Kano.

Mista Peter Obi ya sanar da bada tallafin karatun ne ga Auwalu Salisu a wurin babban taron jagoranci da bada kyaututtuka a Abuja. Da yake maida jawabi bayan ya karbi Lambar yabo a matsayin gwarzon dan siyasa na wannan shekara,Mista Obi yace a shirye yake ya zuba jari a yankin arewacin kasar nan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =