Akwai manyan alamu dake nuni da cewar kungiyoyin kwadago zasu nemi Naira Dubu 500,000 a matsayin mafi karancin albashi yayin da za’a fara taron jin ra’ayin jama’a na shiyya-shiyya dangane da mafi karancin albashi yau a Jihohin Legas, Kano,Enugu,Akwa Ibom,Adamawa da kuma Abuja.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC Joe Ajaero, ya bayyana cewa idan hauhawar farashi ya cigaba a Najeriya kungiyar kwadago ta NLC zata nemi Naira Milyan 1 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata.
Haka kuma shugaban kungiyar yace,la’akari da bukatar da Mambobin suka gabatar daga helkwatar Jihohi, akwai yuyuwar kungiyar NLC ta nemi Naira 500,000 a matsayin mafi karancin albashi a zaman da zasu yi yau.
Za’a gabatar da taron jin ra’ayin jama’a a dukkan shiyyoyi 6 na kasar nan, ana tsammanin zai samu halartar Mambobin kungiyoyin kwadago, gwamnonin Jihohi, Ministoci, kungiyoyin fararan hula da kuma Kamfanoni masu zaman kan su, kan mafi karancin albashi saboda matsalolin tattalin arziki da bukatun ma’aikatan gwamnati.