
Majalisar wakilai ta yi kira ga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro da ya dai-daita ayyukan leken asiri da na hukumomin tsaro a kasar nan, musamman a Jihar Kaduna, biyo bayan sace dalibai kimanin 200 da ‘Yan bindiga suka yi a makon da ya gabata a kauyen Kuriga dake karamar hukumar Chikun ta Jihar.
‘yan majalisar sun nuna damuwa kan kudi Naira Tiriliyan 3.25 da majalisar dokokin kasa ta amince a warewa fannin tsaro da dakarun sojojin Najeriya, amma duk da haka ‘yan kasa basu ga wani cigaba ta fuskar tsaro ba.
Yayinda matsalar tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar nan,Majalisar wakilan ta yi kira da a shawo kan matsalar yaduwar manya da kananan makamai a Najeriya.
Matakin na majalisar wakilai na zuwa ne bayan amincewa da wani kudiri dake neman a gaggauta ceto yaran da aka sace kimanin 200 a garin Kuriga na karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
